Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama Ya Godewa Sojojin Amurka Don Kareta Zamanin Mulkinsa


President Barack Obama yayinda yake jawabi jiya
President Barack Obama yayinda yake jawabi jiya

A jawabinsa na karshe ga kasa a kan tsaro, Shugaba Barrack Obama na Amurka ya godewa rundunar sojin kasar a kan yadda suka tsare kasar.

A cikin jawabin da ya gabatar a Barikin Soja na MacDill dake garin Tempa a jihar Florida, kuma ba tare da ambatar sunan shugaba mai jiran gado Donald Trump ba, Obama ya yi patali da kiran da Trump din ke yi na haramtawa musulmi shigowa Amurka da kuma abubuwan da ya fada a lokacin yakin neman zabe.

Obama yace a lokacin mulkinsa na shekaru takwas babu wata kungiyar yan ta’adda da tayi nasarar kawowa Amurka hari, ya kuma ce ba wai don basu jarraba ba ne.

Kafin jawabin nashi, shugaban ya sadu da hafsoshi da sauran sojojin rundunar tsakiyar kasar inda ya gode musu. Haka kuma Obama ya yi anfani da wannan ziyarar wajen bayyana yadda yake ganin yaki da ta’addanci zai kasance bayan wa’adin mulkin nasa ya kare.

Sojojin da suka dinga tafawa Shugaba Obama yayinda yake gode masu
Sojojin da suka dinga tafawa Shugaba Obama yayinda yake gode masu

Obama ya sami babban tafi a lokacin da yace Amurka ta ga bayan madugun kungiyar al-Qaida, Osama Bin Ladin.

A wani hannunka mai sanda da ya yi tun farko a kan batun haramtawa Musulmi shigowa, Obama yace bai yuwa yaki da ta’addanci ya zama yaki da Musulmi. Yace kare yancin Bil Adama abu ne da aka san Amurka da shi tun ba yau ba.

Wasu masu sukar shirin yaki da ta’addanci na shugaban kasar, ciki har da zababben shugaba Donald Trump sun ce janye sojojin Amurka daga Iraqi da aka yi, Obama ya bar wani gibi da ya ba yan ta’addan damar kafa wani dandali.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG