Bukin wanda aka soma tun shekarar 1978, yana da manufar zaburar da sojoji da kara basu horo na tunkarar yaki, kazalika tare da amfani da na’urorin zamani, shugaba Muhammadu Buhari wanda yayi shigar yaki ne ya kaddamar da soma atisayen.
Ministan tsaro Mansur Muhammed Dan Ali, yace gudanar da atisayen a yankin Dan sadau dake fama da hare haren barayin shanu yana da manufa biyu. Ministan ya bayyana cewa a kowace shekara akan gudanar da wannan atisaye amma wannan ne karo na farko da aka gudanar da shi a jihar Zamfara.
Ya kara da cewa mutanen jihar Zamfara zasu amfana da wannan atisaye domin yazo dai dai da lokacin jama’ar jihar ke cikin halin akuba da barayin shanu da harkar tsaro ta gallabi jihar, domin hakane mai girma shugaban kasa ya ga ya dace aje wannan guri domin a shiga dazuzzukan a bankado duk wadanda suke aikata wannan muguwar barna.
Duk da yake kungiyar Fulani ta miyatti Allah dake jihar ta goyi bayan wannan mataki da gwamnati ta dauka, amma tana fargaba akan lamarin kamar yadda shugaban kungiyar Alhaji Tukur Jan Gebe ya bayyana.
Ya ce “abinda muke tsoro shine, sojojin baki ne dan haka kada su fadawa rugagen filani su hallaka jama’ar da basu jiba basu gani ba”.
A mayar da martani kan tambar da wakilin sashen hausa yayi masa kan cewa ana zargin cewa ana zargin cewa Fulani ne ke aikata wannan barna a dajin na dan sadau, shugaban kungiyar fulanin ya ce babu irin kabilar da babu a cikin masu aikata wannan aika aika.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.