A washegarin harin ta’addancin da ya hallaka sojoji 71 a Barikin Inates na iyakar Nijar da Mali, ‘yan kasar sun fara bayyana matsayinsu game da wannan al’amari da ke ci gaba da daurewa jama’a kai.
Jama'a na dasa alamar tambaya ne bisa la’akari da yadda ‘yan ta’addan suka yi nasarar afkawa wadannan sojoji da rana tsaka.
Shugaba Issouhou Mahamadou, ya jagoranci taron majalisar tsaro ta kasa a fadarsa domin duba hanyoyin da za a bullowa wannan sabon al’amari, wanda ya sa jama'a cikin halin zullumi da juyayi.
A birnin Yamai fadar gwamnati, duk inda ka shiga zancen harin nan a ke wanda a fili ake ganin wannan bacin rai a huskar ‘yan kasa.
Sanarwar da gwamnatin Nijar ta fitar na cewa, harin na ranar Talata, ya janyowa kasar asarar rayukan sojojinta 71, inda 12 suka jikkata, yayin da wasu masu hari suka yi batan-dabo.
Gare Amadou, wani dan jarida mai zaman kansa, ya ce a sake duba tsarin al’amuran yau da kullum domin akwai bukatar aiwatar da canje-canje a sha’anin gudanar da ayyukan tsaron kasar.
Rashin wadatar kayan yaki da ma abin da ya shafi nagartarsu, wani abu ne da ‘yar majalisar dokokin kasa, Hadiza Seini Maiyaki, ta ce abin dubawa ne.
A wani kiran kwantar da hankali, Shugabanin addinai irinsu Ustaz Malam Haja, na cewa a yau alhamis Shugaba Issouhou Mahamadou ya jagoranci taron majalisar tsaro ta kasa a fadarsa domin taya al’umar Nijar juyayin wannan babban rashi.
Kasashen G5 Sahel, sun sauya wurin taron da suka shirya gudanar wa ranar Lahadi mai zuwa a birnin Ouagadougou zuwa birnin Yamai, yayin da kasar Faransa ta dage nata taron zuwa farkon shekarar da zamu shiga.
Har zuwa yanzu ba wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan hari,.
Sai dai ana kyautata zaton hadin gwiwar kungiyar Ansardine da Aqmi da Almurabitun a karkashin jagorancin Iyad AgGhali ne ke da hannu a wannan aika aika.
Akwai alamu da ke nuni da cewa, harin ba zai rasa nasaba da Abu Whalid Alsarahui na reshen IS a yankin Sahara ba a bisa la’akkari da yawan maharan da suka afkawa barikin sojan na Inates.
Ga rahoto cikin sauti.
Facebook Forum