Bisa ga kiraye kiraye da dubban jama’ar Najeriya sukayi masa na cewa ya fito ya nemi wannnan mukami a dai dai wannan lokaci.
Sai dai ana cigaba da babbar takaddama da kalubale dangane da yanke shawarar gudanar da wannan bukin a daidai wannan lokaci da aka rasa rayukan wadansu ‘yan makaranta su sama da arba’in, yayinda kusan dari aka kwantar dasu a asibiti a wani bom da aka tada a wata makarantar sakandare dake Fataskum a jihar Yobe.
Shi kanshi shugaban kasar alokacin da yake gabatar da kansa cewar asake zabensa a matsayin shugaban kasa, yayi juyayi akan rashin wadannan daliban, dakuma bada karfin gwiwa ga al’ummar kasar Najeriya cewar za’a dauki matakai na tsaro da kara yawan kayan aiki domin tabbatar da cewar an yaki wannan matsala ta ta’addanci acikin dan karamin lokaci. Ya dai bayyana irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu a wurin gudanar da ayyuka na raya al’umma, raya kasa da kuma cigaban al’umma baki daya.