Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi kasar Rasha da taimaka ma kasar Koriya Ta Arewa da dabarar tsallaka takunkumin da duniya ta kakaba ma ta, ya kuma ce kulluyaumin Koriya Ta Arewar na ci gaba da samun nasara wajen kera makami mai linzaminta mai iya isa Amurka.
A wata hirar da ya yi da kafar labaran Reuters a fadarsa ta White House, Shugaba Trump ya yaba ma kasar China saboda kokarin da ta ke yi wajen takaita yawan man fetur da gawayin ‘coal’ da ake samar ma Koriya Ta Arewa, to amma ya ce ya kamata China ta kara azama wajen taka ma Koriya Ta Arewar burki. Ya kuma ce da alamar kasar Rasha na cike gibin da China ta bari na taimaka ma Koriya Ta Arewar.
Trump ya ce mai yiwuwa Shugaban Rasha na yin kafar ungulu ga takunkumin da aka sakawa Koriya ta Arewa din da gangan.
A yayin hirar ta tsawon sa’a guda, Trump bai nuna kwarin gwiwa kamar yadda ya nuna kwanan baya ba, kan cewa zai tattauna da Shugaban Koriya Ta arewa Kim Jong-Un kai tsaye ba.
Da ‘yan jarida su ka tambaye shi ko ya tattauna kai tsaye da Kim, Trump bai yi wani takamaiman bayani ba. To amma ya ce ya na iya tattaunawar fuska-da-fuska da Shugaban na Koriya ta Arewa.
A halin da ake ciki kuma, yayinda likitocin Shugaban Amurka Donald Trump fahimtar al’amurra, a gwajin da aka masa ranar Talata, wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa mafi yawan Amurkawa na ganin Trump bai da natsuwa.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Jami’ar Quinnipiac ta gudanar ta nuna cewa kashi 45% na masu kada kuri’a na ganin Trump na da natsuwa, a yayin da kuma kashi 47% ke cewa bai da natsuwa.
Kuri’ar ta kuma nuna cewa akasarin maza na ganin Trump na da natsuwa, a yayin da kuma akasarin mata ke ganin bai da natsuwa.
A satin da aka ba da rahoton cewa Trump ya yi amfani da kalaman batunci kan ‘yan kasashen Haiti da El Salvador da Afirka da ke shigowa Amurka, kuri’ar ta nuna kashi 59% na Amurkawa masu kada kuri’a sun yi imanin cewa Trump ya fi mutunta farar fata fiye da sauran mutanen dake da wani launin fata.
A takaice dai kuri’ar ta Jami’ar Quinnipiac ta nuna cewa kashi 38% na masu kada kuri’a ne kadai su ka amince da salon mulkin Shugaban.
Facebook Forum