Ranar Juma’a ne Trump ya ce wannan shine karo na karshe da zai janye daga sakawa Iran takunkumin da Amurka ta amince ‘dagewa karkashin yarjejeniyar shekarar 2015, domin baiwa ‘yan Majalisa da kasashen Turai kwanki 120 su samu hanyar gyara abin da ya kira “ábubuwan da suka lalace” a cikin yarjejeniyar.
Lavrov ya fadi jiya Litinin cewa idan har Trump ya ci gaba da aiwatarda abubuwan da yake barazanar yayi na ficewa daga yarjejeniyar, akwai mummunan sakamako da ka iya biyo baya, tunda ba shakka Iran zata daina aiki da ka’idojin yarjejeniyar.
Amurka da Rasha da Birtaniya da China da Faransa da kuma Jamus sune suka hada kai suka samar da yarjejeniyar domin tabbatar da ganin cewa Iran bata ci gaba da shirin Nukiyarta ba wajen yin makamai. Iran dai ta nace cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne.
Facebook Forum