Amurka ta sake sanya takunkumin karya tattalin arziki akan Iran wanda a baya ta taba sanyawa don hurawa kasar lamba akan takaita shirin ta na Nukiliya, amma daga baya aka dage a karkashin wata yarjejeniya da aka cimma a shekarar 2015.
Shugaba Donald Trump ya sha sukar wannan yarjejeniyar ya kuma fidda Amurka daga ita watanni 3 da suka gabata, abinda ya janyo sake maida takunkumin wanda ya fara aiki a daren jiya litinin.
Trump ya rubuta a shafin sa na twitter yau Talata cewa “an sake sanya takunkumi akan Iran a hukumance.” Wannan shine takunkumi mafi tsanani da aka taba sanyawa, kuma a watan Nuwamba matakin zai kara tsanani. Duk mai huldar kasuwanci da Iran ba zai yi wata harkar kasuwanci da Amurka ba. kwanciyar lafiyar duniya kawai mu na ke buakata, ba wani abu ba, a cewar Trump.
Takunkumin da aka sanya zai auna bangaren kamfanonin motocin Iran, da harkar kasuwancin gwal, da wasu abubuwan masu martaba na kasar, da kuma harkokin kudaden kasar.
Facebook Forum