Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Dauke Fiye Da Mutane 1,000 Bayan Wata Girgizar Kasa A Indonesia


An fara kokarin dauke fiye da mutane 1,000 da suke yawon bude ido daga wani tekun Indonesia kwana daya bayan wata girgizar kasa da ta auku, ta kashe akala mutane casa'in da takwas, tare da raunata fiye da mutane 200.

Hukumar nazarin yanayi ta Amuraka tace girgizar kasar ta kai karfin maki bakwai, kuma ta afku ne a kimamin kilomita goma da rabi a arewacin tsibirin Lombok. Haka kuma an ji duriyarta ko kuma hushinta a tsibirin Bali da Sumbawa da kuma wasu yankunan gabashin Java.


Mai magana da yawun hukumar shawo kan matsalar bala'oi Sutopo Purwa Nugroho ya fadawa manema labarai cewa, barnar tayi muni ainun, kuma ana cigaba da kokarin gano mutane tare da dauke mutane daka tekun. Ya kara da cewa agajin da suke amfani da shi yayi kasa sosai.

Abin da aka fi bukata a wannan lokacin, shine, ma’aikatan lafiya,da magunguna, da abinci, mussamam ma abincin da za’a iya amfani da shi yanzu. Muna bukatar su da yawa saboda mutane da dama sun zama kamar yan gudun hijira kuma sun bazu ko ta ina a yankin. Nugroho yace ana kyautata addadin mutanen da suka mutu zai karu, yayin da tawagar su ke cigaba da gano mutane a yakunan da abin ya shafa.’’ Ya ce a cikin waddanda suka mutu babu wandada suka zo yawon bude ido.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG