Tace makasudin yin hakan shine ta tantance koda gaske ne rahoton nan da ke cewa harin da aka kai ya kashe fararen hula har sama 100, inji mai Magana da yawun rundunar.
Yace “muna kokarin gane gaskiyar wannan batu ne, inji kanar JohnThomas, mai Magana da yawun rundunar sojojin tsakiya ta Amurka, wanda sune ke kula da ayyukan rundunar sojojin Amurka dake aiki a gabas ta tsakiya, yace wannan shine babban abinda yake da muhimmaci a gare mu yanzu game da Mosul”.
Sai dai ma’aikatar tsaron Amurka, wato, PENTAGON, tace kashe fararen hula a arewacin Iraqi, a birnin Mosul, sakamakon wannan harin wani babban abin takaici ne.
Ministan tsaron Amurka, Jim Mattis, ya fada jiya litini cewa ba wata rundunar sojan duniya data nuna damuwar ta akan halin da fararen hula suka shiga, yace sau tari Amurka, tana iya bakin kokarin ta domin ganin an rage hasarar rayukan bayin ALLAH da basu ji ba basu gani ba lokacin duk wani hari da Amurka, keda hannu a ciki.
Facebook Forum