Yayinda shugaban Amurka Donald Trump ke tunanin yiwuwar daukar matakin soja akan Koriya ta arewa, dakarun Amurka sun nunawa Koriya ta arewa hazakarsu.
Manyan jiragen sama masu sakin bomabomai sun hadu da jiragen saman Koriya ta kudu da na Japan inda suka yi wani atisaye, suka harba makamai masu linzame daga gabashi da kuma yammacin gabar zirin Koriya.
Wannan atisayen na faruwa ne yayinda Trump da masu bashi shawa suka gana da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger, a lokacin da shugaban ya bayyana sabuwar hanyar tunkarar Koriyar ta arewa.
Shugaba Trump ya ce, da muna kan hanyar da ba ta dace ba. Abinda zaku yi shine ku duba da kyau. Idan ku ka yi nazarin shekaru 25 da suka wuce, muna kan hanyar babbar matsala da gwamnatocin baya suka sanya Amurka a ciki, matsalar da duniya bata taba ganin irin ta ba, amma yanzu muna kan hanyar data dace.
Facebook Forum