Shugabannin yankin Catalonia masu tsautsauran ra’ayin a ware, sun yi kememe sun ayyana yankin a matsayin mai cin gashin kansa, amma kuma sun ce ba za su fara aiwatar da shirin ballewar ta su ba, domin suna so su ba da kofar tattaunawa da gwamnatin Spain.
Yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin yankin na Catalonia, shugaban majalisar, Carles Puigdmont, ya yi kira ga hukumomin Madrid da su shiga tattaunawar, inda ya kara da cewa yankin ya cancanci samun ‘yancin kansa.
Wani kakakin gwamnatin Spain ta Firay Minista Mariano Rajoy, ya ce gwamnatin ta yi wancakali da ayyana ballewar da yankin daga kasar.
Kakakin ya kara da cewa, ai babu batun tattaunawa kuma, tun da shugabannin yankin na Catalonia sun riga sun ce suna son su balle.
A daren jiya Talata Puigdemont, ya kara tabbatarwa ‘yan majalisar dokokin yankin cewa, Catalonia zai bi tafarki ko kuma tsarin mulkin Jamhhuriyya ne.
Facebook Forum