Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Lantarki ta Wadata a Legas


Wayoyin wutar lantarki
Wayoyin wutar lantarki

Rashin wutar lantarki a kowane babban gari a Najeriya ba labari ba ne. Samun wutar lantarki a kowane lokaci a babban birni kaman Legas shi ne babban labari

Tun da sabuwar gwamnatin Buhari ta kama aiki aka soma samun wutar lantarki na tsawon lokaci a Legas sabanin yadda aka saba gani.

Wani mai sana'ar aikin aski a birnin Legas ya bayyana cewa makonni biyu ke nan bai tada janareto nashi ba saboda akwai wutar lantarki koyaushe a birnin dake zama cibiyar kasuwancin yammacin Afirka.

Yanzu haka dai wutar lantarki dake zama turaren dan goma ga al'ummar Najeriya za'a iya cewa an kama hanyar samunsa ba dare ba rana. A wasu unguwannin birnin ana samun wutar sa'o'i 24 babu ko kibta ido.

A makon jiya ne dai hukumar samarda wutar lantarki ta kasa ta sanarda samun megawats fiye da 4,600 na wutar.

Wakilin Muryar Amurka a Legas ya zagaya birnin domin tabbatar da ikirarin wadatar wutar lantarkin.

Wadanda suka gani a kasa sun tabbatar da hakan. Wani tela da a da ya dogara ga anfani da janareto mai samar masa da wutar lantarki Malam Bashir yace wuta yanzu tubarkalla sai hamdala. Akwai banbanci sosai tsakanin da da yanzu. Yanzu wuta tana kwana ta wuni ba tare da an dauketa ba. Da akan yi sati guda ma ba'a ga wuta ba.

Mutanen birnin Legas na bayyana mamaki da samun wutar lantarki watanni biyu da samun canjin gwamnati.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Shiga Kai Tsaye


.

XS
SM
MD
LG