Lokacin neman zabe shugaba Buhari ya yi alkawarin daukan matakan da zasu inganta rayuwan 'yan Najeriya.
Yau Laraba shugaban ya amince da daukan matakan gaggawa na aiwatar da shirin Majalisar Dinkin Duniya na tsaftace muhallai da kasar ta yi watsi dasu da can baya.
Bisa ga umurni da shawarwarin da daraktan tsaftace muhalli na Majalisar Dinkin Duniya ko UNEP da wakili na musamman na kasar Ogoni da manyan sakatarorin ma'aikatun tsaftace muhali da na albarkatun man fetur da masu ruwada tsaki shugaban ya amince da gyaran fuskar da aka yiwa shirin HYPREP .
Biyo bayan amincewarsa ya kafa kwamitoci biyu masu karfin iko. Daya na zartsawa daya kuma na amintattu.
Kwamitin zartaswa zai kunshi wakilai daga ma'aikatun man fetur da na tsaftace muhalli da jihohin da man fetur ko hakan ma'adanai suka gurbata muhallansu da kamfanonin mai tare da NNPC da wakilin Ogni da Majalisar Dinkin Duniya.
Shi ma kwamitin amintattu ya hada da gwamnatin tarayya da NNPC da kamfanonin man fetur na kasashen waje da wakilin Ogoni da Majalisar Dinkin Duniya.
Shugaban ya bada umurnin a fara tara kudi dalar Amurka miliyan goma kwana talatin bayan an kaddamar da kwamitin amintattu wanda zai tara kudin daga masu bada tallafi.