Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bola Tinubu Ya Nada Malam Nuhu Ribadu, Darazo, Alake, Edun A Matsayin Masu Ba Shi Shawara.


Shugaba Tinubu
Shugaba Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana nadin mukamai na musamman guda takwas, kamar yadda wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Najeriya Abiodun Oladunjoye ta bayyana.

Daga cikin sabbin mashawartan da aka nada akwai Malam Nuhu Ribadu, wanda fitaccen mutum ne a fannin tsaro a Najeriya kuma shugaba na farko a hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC. Malam Ribadu zai kasance mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro. Kwarewar Ribadu a fannin bin doka da oda zai taimaka wajen samar da ingantattun tsare-tsare don tabbatar da tsaro da kare al'ummar Najeriya baki daya.

Nuhu Ribadu
Nuhu Ribadu

Sai kuma Mista Dele Alake, wanda zai kasance mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa, da dabaru.

Dele Alake
Dele Alake

An nada Ya'u Darazo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci. A wannan rawar da zai taka a gwamnatin Tinubu, ana bukatar Darazo zai ba da shawarwari masu muhimmanci game da al'amuran siyasa da haɓɓaka kyakkyawar dangantaka da matakan gwamnati dabam-dabam.

Yau Darazo
Yau Darazo

Mista Wale Edu, zai karbi mukamin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudi.

An kuma nada Mrs. Olu Verheijen a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan makamashi/lantarki. Saboda kwarewarta a fannin makamashi, za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance kalubale da damarmaki da suka shafi bukatun makamashin Najeriya da kuma kawo sauye-sauyen da za su kai ga zuwa hanyoyi masu dorewa.

Bugu da kari, an nada Mista Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga.

Sai kuma Mista John Ugochukwu Uwajumogu, wanda zai rike mukamin mai ba da shawara na musamman kan harkokin masana’antu, kasuwanci, da zuba jari. Kwarewar Uwajumogu za ta kasance mai muhimmanci wajen haɓɓaka ci gaban masana'antu, jawo jari, da haɓɓaka harkokin kasuwanci a Najeriya.

Daga karshe an nada Dr. Salma Ibrahim Anas, a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin kiwon lafiya.

Aikin da ta yi a fannin kiwon lafiya da kula da lafiyar jama'a za su taimaka wajen tsara manufofi don magance kalubalen kiwon lafiyar al'umma da inganta samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.

Zabar mashawarta da shugaba Tinubu ya yi na nuni da yadda ya himmatu wajen hada gungun mutane kwararru da gogewa a fannoni dabam-dabam, da nufin magance muhimman batutuwan da ke fuskantar al’ummar kasar.

Wadannan nade-naden na kuma nuni da wani muhimmin mataki na tsara manufofin gwamnati da dabarun tafiyar da harkokin gwamnatin Tinubu.

Babu shakka sabuwar tawagar ta masu ba da shawara za ta fuskanci babban kalubale, amma ana sa ran kwarewar su da kwazon su za su ba da gudummuwa mai kyau ga ci gaba da ci gaban Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Tinubu.

~ Yusuf Aminu

XS
SM
MD
LG