Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Samar Da Bashi Ga Dalibai Ba Tare Da Biyan Kudin Ruwa Ba


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima Da Shugbaan Majalisar Dattawa Ahmed Lawal a bikin ranar dimokuradiyya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima Da Shugbaan Majalisar Dattawa Ahmed Lawal a bikin ranar dimokuradiyya

A cigaba da daukar matakai da sabuwar gwamnatin Najerita ke yi da zummar, abin da ta kira, kyautata makomar 'yan kasar, ta amince da dokar bayar da bashin dalibta ba tare da kudin ruwa ba

A wani mataki da sabuwar gwamnatin Najeriya ta ce na bukasa imili ne ta hanyar bayar da damarmaki ga dalibai masu niyyar shiga manyan makarantun Najeriya, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu (GCFR) ya rattaba hannu kan dokar bada bashi ga dalibai ba tare da kudin ruwa ba.

Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu

Kudirin dokar shi ne samar da sauki ga dalibai 'yan Najeriya don samun damar zuwa manyan makarantu daga Asusun Ilimi na Najeriya ba tare da kudin ruwa ba.

-Yusuf Aminu

XS
SM
MD
LG