Ko da yake, ba za a iya fayyace nasarorin da shugaban ya samu a tsawon kwana 100 na gwamnatinsa ba a bisa la’akkari da ayyukan da ya sha alwashin gudanarwa a tsawon shekaru 5 din da ya kamata ya yi akan karaga, magoya bayan jam’iyyar PNDS Tarayya irinsu Adamou Manzona alfahari da abubuwan da suka wakana a tsawon wannan lokaci.
Wani abin da ba kasafai ake samunsa ba a kasashen Afrika ‘yan adawa kansu na ganin alamun sauyi a tsawon kwanaki 100 na kamun ludayin shugaba Mohamed Bazoum idan aka kwatanta da abubuwan da suka wakana a zamanin shudediyar gwamnatin Issouhou Mahamadou inji Bana Ibrahim na jam’iyar Moden Lumana.
A cewar jam’in fafutuka na kungiyar FSCN Abdou Elhadji Idi yaki da ci hanci da farautar mahandama dukiyar jama’a da ake ganin shugaban na da kyakkywar niyya akansu da kuma dagewarsa akan batun tsaro wani yunkuri ne da ya kamata a yaba da shi idan aka yi waiwaye akan abubuwa da suka faru a shekarun baya.
Shugaba Mohamed Bazoum wanda ya karbi madahun iko a ranar 2 ga watan Afrilun da ya shige ya yi fama da kalubale mai tarin yawa kafin ya dare kujerar shugabancin kasa sai dai kuma makwani 2 bayan haka a fili ‘yan kasa ke nuna gamsuwa da salon mulkinsa a bisa la’akari da wasu sauye sauyen da ya aiwatar
Koda yakejam’iyar PNDS a wata sanarwar da ta fitar a jiya lahdina cewa yabon da Bazoum ke samu daga wajen ‘yan kasa musamman ‘yan hamayya yunkuri ne na neman haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou da shugaba mai ci Bazoum Mohamed.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: