Shugaban ya nada ‘yar tasa bayan da ya kori dukkanin mambobin kwamitin din kamfanin a watan Aprilu.
Isabel wacce ta ke ikrarin ta yi fadi tashi wajen zama hamshakiyar mai kudi, ta kasance mace mafi arziki a nahiyar Afrika, inda ta mallaki dala biliyan 3.3, kamar yadda mujallar Amurka ta Forbes ta bayyana.
Kakakin jam’iyar ta UNITA, Alcides Sakala, ya ce wannan nadi da shugaba ya yiwa ‘yar sa, wata alama ce ta nuna fifiko da badakala da jam’iya mai mulki ta MPLA ta ke yi a kasar.
Ya kara da cewa, sam basu yi mamaki da nadin ba, duk da cewa abin ya basu kunya, kuma hakan ya kara jaddada abin da su ke fadi.
Sai dai magoya bayan jam’iyar ta MPLA, sun ce suna ganin Isabel ce kadai wacce za ta iya kawo sauyi a kamfanin man kasar da ya ke cikin wani hali mara kyau.