Majalisar ta bayyana hakan ne yayin da ake shirin cika shekaru biyar da barkewar yaki a Kudancin yankin na Kordofan.
Gabanin bikin murnar samun ‘yancin kan kasar Sudan ta Kudu ne, yakin ya barke tsakanin gwamnatin Sudan da ‘yan tawayen Sudan People’s Liberation Movement.
A cewar kakakin hukumar ta Majalisuar Dinkin Duniya, Adrian Edwards, a wannan shekarar, fiye da ‘yan gudun hijra dubu 7,500 suka tsallaka kan iyakar kasar zuwa Yida da ke jihar Unity a Sudan ta Kudu.
Ya kara da cewa ana kuma tunanin wasu dubban mutane za su isa yankin a ‘yan makwanni masu zuwa yayin da rikicin na Kudancin Kordofan ya ke kara kazancewa.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan kashi 90 na ‘yan gudun hijra da ke neman mafaka mata ne da yara, inda hukumar ta kara jaddada cewa an raba yara da dama da iyayensu.