Ministan tsaron kasar, Abdulrasaka Omar Mohammed ., ya gayawa Muriyar Amurka cewa, jami'an tsaro sun kashe 'yan bindigar uku lokacinda suka yi musayar wuta a safiyar jiya Alhamis a O'tel din da a ke kira Ambassador, suka kubutar da mutane 57, da 'yan binidgar suka yi garkuwa da su. Harin da aka kai a daren Laraba daga bisani 'yan binidgar suka shiga O'tel din suka yi bude wuta.
Kungiyar al-shabab ta dauki alhakin kai wannan hari, tace ta auna O'tel din ne domin jami'an gwamnatin kasar suna yawan amfani da shi.
Harin da kungiyar ta kai ranar Laraba, ta kai shi ne sa'o'i bayan da jami'an kasar suka bayyana cewa an kashe wani kwamandan kungiyar ta al-shabab a matakin da sojojin kasa suka kai a kudancin kasar. Ana zargin wanda aka kashen Mohammed Mahamud, wanda ake zargi a zaman wanda ya kitsa harin da aka kai kan wata kasuwar zamani da kuma jami'ar Garissa inda mutane 148 suka rasa rayukansu duk a Kenya.