Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Habbaka Kudancin Sudan


’Yan Kudancin Sudan ne ke jiran abinci, da wuraren kwana, da yanayin tsaro da kuma magunguna a kauyen Nzara, da ke dab da kan iyakar Sudan da Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo.
’Yan Kudancin Sudan ne ke jiran abinci, da wuraren kwana, da yanayin tsaro da kuma magunguna a kauyen Nzara, da ke dab da kan iyakar Sudan da Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo.

Gwamnatin Kudancin Sudan za ta maido da ‘yan yankin don su yi zaben raba gardama.

Gwamnatin Kudancin Sudan ta tsara yadda za ta maido da ‘yan yankin su kimanin miliyan daya da rabi da yaki ya kora su zuwa Arewacin kasar don su ma su kada kuri’unsu a zaben raba gardamar nemar ‘yancin kai da za a yi a watan Janairu.

Shirin na gwamnati, wanda aka bayyana wa manema labarai a wannan satin, an masa taken “Zuwa Gida Don Yin Zabe.” Shugabannin Shirye-shiryen sun hada da tsarin maido da mutane ta jiragen kasa, da bas-bas, da kuma jiragen ruwa da za su bi ta Kogin Nilu.

Harotanni sun banbanta kan kudin da aka kasafta, to amman ba zai gaza dala miliyan 25 ba.

Gwamnatin Kudancin Sudan ta ce ta damu saboda yiwuwar ‘yan Kudanci su fuskanci matsaloli a lokacin zaben na raba gardama da za a yi ran 9 ga watan Janairu da kuma bayan zaben.

To amman kungiyoyin agaji su ka ce suna fargabar yiwuwar kwararowar dinbin jama’a kwatsam ta jefa yankin da ke fama da karancin abinci cikin matsanaciyar wahala, musamman ganin har yanzu yankin bai murmure ba daga yakin basasan tsawon shekaru 21 tsakanin Arewa da Kudu.

XS
SM
MD
LG