Tsagera masu alaka da kungiyar al-Qa’ida sun dauki alhakin harin da aka kai jiya talata kan wani hotel a Somaliya, inda aka kashe mutane 31, cikinsu har da ‘yan majalisar dokokin Somaliya su 4. Kungiyar tsagera ta al-Shabab, wadda ke rike da sassa masu yawa na kasar Somaliya, ta ce ta kai wannan farmakin ne a kan ‘yan majalisar dokokin Somaliya dake zaune a hotel din.
Kakakin al-Shabab, Ali Mohamud Rage, yace a cikin sauki, zaratan sojojinsu sun samu shiga cikin wannan hotel mai suna Muna dake unguwar Hamarweyne da gwamnati take rike da shi. Ya ce, "mayakan al-Shabab sun shiga hotel din dake kusa da fadar shugaban kasa a cikin sauki. Sun kashe kusan dukkan ‘yan majalisar dokokin dake cikin hotel din."
Shaidu na gani da ido dai sun fadawa VOA cewa wasu ‘yan bindiga su uku da suka yi shiga kamar sojojin gwamnati, sun harbe masu gadi biyu a kofar hotel din suka kutsa ciki. Daga nan suka fara bi daki-daki su na harbin duk wanda suka gani, kuma da harsasansu suka kare sai suka tayar da bama-baman dake jikinsu.
Mutane 31 suka mutu a wannan zub da jini, cikinsu har da ‘yan majalisar dokoki 4. Wasu ‘yan majalisar su 5 sun ji rauni.
Hotel din Muna yana kusa da fadar shugaban kasa a cikin bangare kalilan na Mogadishu da har yanzu yake hannun gwamnati.
Amurka ta fito da kakkausar harshe tana yin Allah wadarai da wannan harin. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, P.J. Crowley, yace kai wannan harin a cikin wata mai tsarki na Ramadhan ya nuna yadda kungiyar ta al-Shabab ba ta mutunta ran dan adam, ko al’adun kasar Somaliya ko kuma addinin Islama.
Shi ma babban mai ba shugaba Obama shawara kan yaki da ta’addanci, John Brennan, yayi tur da wannan hari na al-Shabab, inda ya ce, "wannan harin abin yin Allah wadarai ne musamman ma a watan mai tsarki ga Musulmi na Ramadan. Irin akidar da al-Shabab take da niyyar kafawa a Afirka ta sha bambam baki daya da irin akidar mafi yawan al’ummar wannan nahiya."