Shugabannin Kudancin Sudan sun gabatar da wata katafariyar taswira ta sake gina manyan birane biyu da siffofin wasu sanannun dabbobin Afirka akan kudi dala miliyan dubu 10. Bayanan taswirar da aka nuna yau Alhanis sun nuna za’a canza wa babban birnin Kudancin Sudan, Juba, wuri kuma a sake gina shi da siffar rhinoceros (Gwanki). Sannan kuma birni na biyu a girma a yankin, Wau, za a gina shi da siffar rakumin daji.
Jami’an basu fadi yadda za su samo kudin yin wannan aikin ba. Dala miliyan dubu 10 dai ya ribanya kasafin kudin gwamnatin na shekarar 2010. Shi dai wannan yanki mai kwarya-kwaryar yancin gashin kai, wanda kuma ke shirin gudanar da zaben raba gardama game da ‘yancin kai a watan Janairu mai zuwa, na da dinbin albarkatun man fetur. To saidai yau shekaru biyar ke nan da kawo karshen yakin basasa tsakanin yankin da Arewacin kasar, amman har yanzu yankin na fama da rikice-rikicen kabilanci da kuma karancin abinci.