Cikin kasafin kudin kasar na wannan shekara ta 2016, an ware kimanin Naira bilyan dari hudu da talatin da uku ga ma'aikatar ayyuka, Gidaje da makamashi. kuma za a kasha kimanin kashi goma sha biyar na kasafin a aikin samar da gidajen. kamar yadda alkaluma su ka nuna za a samar da gidajenne a daukacin shiyyoyin kasar daban daban.
Ma'aikatar ayyukan kazalika zata samar da hanyoyi da magudanan ruwa a Oron na jihar Akwa Ibom, Keffin jihar Nasarawa, da Nkwubor na jihar Enugugu akan kudi Naira milyan dari biyar da arba'in kana za a kamala aikin gina gidaje na tarayya a sulejan jihar Niger, aikin ana sa ran zai lashe zunzurutun kudi har Naira sama da milyan dari takwas.
Masu sharhi na kallon wannan yunkuri ta fuskoki daban daban, wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma kwararren dan jarida Mallam Hassan Gimba Ahmed yace gidajen da gwamnatin tarayya zata gina a suleja ya na da matukar mahimmanci domin daya bisa uku na ma"aikatan dake Abuja a sulejan suke da zama don haka wannan babban abin a yaba ne.
Injiniya mohammed kyari sandabe da yayi fice a sha"anin hada hadar gidaje a Abuja yace yana da kwarin gwiwar a wannan karo ma"aikatar ayyuka ta kasar zata yi rawar gani duba da yadda aka sa azamar cimma muradun kawo canji na shugaba muhammadu Buhari.