A wata hira da ta yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Turai ta ce ita ba ta san inda labarin ya samo asali ba.
Wasu kafofin yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa iyalan tsohon shugaban kasar suna korafin cewa an manta da su, amma Turai ta ce labarin ba shi da tushe ballantana makama.
“Wallahi ba ni na yi ba, ni ban taba hira da kowa ba, kuma ban yi magana da kowa ba.” Inji Turai.
Turai ta kara da cewa, babban abu garesu shi ne duk inda ta ratsa sai mutane sun yi ta ma mai gidanta addu’a, saboda haka ba su da ra’ayin cewa an manta da su.
“Ka wuce a yi ma mutum addu’a a ce Allah ya ji kan Mutawalle shine babban abu, mu bamu da wani korafi Alhamdulillahi, mun gode wa Allah.” Turai ta ce.
saurari cikakkiyar hirar Hajiya Turai 'Yar'adua da Aliyu Mustapha na Sokoto: