Abubakar Shekau ya aika da sakon tsawon minti goma da 'yan kai cikin harsunan Hausa da Larabci inda ya kushewa nadin da sugabanin ISIS suka yiwa Abu Musab al-Barnawai a matsayin sabon shugaban kungiyar Boko Haram.
Abubakar Shekau ya nuna yana nan kan mukaminsa na jagorancin 'yan Boko Haram da zayyana al-Barnawi a matsayin kafiri domin, wai, muradunsu ma sun sabawa juna.
Wani Danlami Dan Maliki dake Maiduguri ya bayyana yadda birnin ke ciki da fitowar sakon Abubakar Shekau. Yace a Maiduguri suna ganin lamarin duk ba zai wuce wata farfaganda ba. Sun ce da Shekau ko babu shi, sun ga cigaba a kokarin karya lagon kungiyar. Kungiyar ta zo karshe.
Wasu kuma suna mamaki cewa har yanzu akwai sauran 'yan ta'adan ba'a samu an kakkabesu ba har ma suna tunanen canza shugabanci!
Mutane basu firgita ba a Maiduguri saboda fitowar sabon sakon.Mutane nada karfin gwuiwar an samu zaman lafiya.
Dr. Muhammad Bello na Jami'ar Jigawa, masanin harkokin ta'adanci na kasa da kasa yace dambarwar da aka samu tsakanin 'yan Boko Haram baraka ce sanadiyar nasarorin Najeriya da na gamayyar kawancen ksashe.Yanzu an samu barakar shugabanci da akida.
Barakar zata ba sojojin Najeriya nasara sosai saboda kungiyar Boko Haram yanzu bata da kwanda daya.
To saidai rundunar tsaron Najeriya tace da Shekau ko babu muradunsu shi ne su kakkabe buraguzai da burbudin 'ayan ta'adan
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.