Shirin wanda ke karkashin kulawar rundunan sojin kasar, zai hada da kungiyoyi daban daban har goma sha hudu, da suka hada da na kwararrun da zasu koyawa tubabbun sana’o’i da kuma malaman addinai.
Bayan da aka duba cibiyar da za a tsugunnar da tsoffin ‘yan Boko Haram din, kwamanda mai kula da shirin Birgediya Janal Bamidele Shafa, yace shirin mai lakabi da sunan “Operation Safe Corridor” wanda gwamnatin tarayya ta tsara hanya ce madaidaiciya domin sauyawa tsoffin ‘yan kungiyar Boko Haram din tsatstsauran ra’ayi da kuma shiryar da su zuwa ga mutanen kirki.
Tawagar dai ta kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dan Kwambo, inda ya jaddada musu samun goyon bayan gwamnatocin jihohin Arewa maso Gabas, domin cimma burin shirin da zai kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Gwamnan ya bukaci jama’a da su saka ido sosai kan abin da suka gani ba su amince ba, su kuma kai rahoto gun jami’an tsaro.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta ‘kasa NEMA, Mallam Sani Sidi, yace wannan abu ba sabon abu bane, wanda yanzu haka an tanadi abinci da za a rika ciyar da tubabbun ‘yan Boko Haram din. Ana sa ran za a tsugunnar da tsaffin ‘yan kungiyar Boko Haram din kimanin guda 800, na tsawon lokacin da ba fayyace ba a yanzu haka.
Domin Karin Bayani.