Bayan sanarwar, kawo yanzu an kashe mutane da dama tare da sace mata fiye da sittin.
Wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya sake tuntubar Danladi Ahmadu wanda ya kira kansa sakataren kungiyar Boko Haram ta zahiri.
Da aka fada masa cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun cigaba da kai hare-hare da sace mata a Waga Mangoro cikin jihar Adamawa da wasu yankunan Borno sai Danladi yace su basu da masaniya. Wadanda suka kai hare-haren ba 'yan kungiyarsu ba ne na zahiri. Yace zasu bincika.
To saidai mutanen kauyukan da lamuran suka shafa sunce an yanka mazajensu. An sace wasu mata. An kone gidajensu tare da rusa ko kone wuraren ibada. An kuma sace masu abinci.
Sabili da abubuwan dake faruwa mutane basu yadda an tsagaita wuta ba. To saidai Danladi yace tana yiwuwa barayi ne. Idan kuma 'yan kungiyarsu ne to watakil basu da labarin yarjejeniyar da aka cimma.
Danladi yayi alkawarin bin digdigin abubuwan da suka faru kana su san abun da zasu yi.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.