Majalisar wakilan Najeriya ta bi sawun ‘yan’uwanta dake majalisar dattawa, inda ta amincewa shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ci bashin kudi dala biliyan daya, domin magance matsalolin tsaro da kasar ke fama da su shekaru biyar Kenan.
A ta bakin dan majalisa Mohammad Ummaru Bago, yace sun amince da bukatar sayen makaman ne don sabodo kada gobe a yi kuka da su. Ma’ana kada ace sune suka hana a yaki ‘yan Boko haram.
Wata majiya kwakkwara da ta so a sakaya sunanta, ta fada wa muryayr Amurka cewa, ba a sami Kashi biyu cikin ukkun ‘yan majalisar da ake bukata ba a lokacin da aka aiwatar da kudirin.
Shi kuma dan majalisar Ibrahim El-sudi, daga arewa maso gabashin Najeriya, yankin da ta’addancin yaki ci yaki cinyewa yace babu laifi idan dai za a yi amfani da kudin akan abinda aka kudura. Amma idan ba a yi hakan ba to lallai an zalunci ‘yan Najeriya.
Alkaluma sun ruwaito cewa ya zuwa yanzu, mahukuntan Najeriya sun kashe kudi kusan triliyan 5 akan batun tsaro. Abin fata dai shine kwalliya ta biya kudin sabulu.
Kamar yadda za kuji a nan, ga rahoton daga Madina Dauda wakiliyar muryar amurka a birnin tarayya Abuja.