Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me ‘Yan Najeriya Ke Cewa Game Da Wa’adin Kama Shekau?


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

A karshen makon da ya gabata, babban Hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya baiwa kwamandan yakin "Operation Lafiya Dole" Manjo Janar Ibrahim Attahiru, wa'adin kwanaki 40 ya kawo mai shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a raye ko a mace, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya musamman ma a tsakanin masana.

Tun bayan da babban Hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ba kwamandojin dakarunsa wa’adin kwanaki 40 su nemo shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a raye ko a mace al’umar kasra musamman masana harkar tsaro suke ta tofa albarkacin bakinsu.

Yayin da wasu ke maraba da wannan mataki na wa’adin kama Shekau, wasu kuwa suke ya kamata a yi hattara

A karshen shekarar 2016, rundunar sojin Najeriya ta ayyana nasarar fatattakar mayakan Boko Haram daga dajin Sambisa, maboyar da ake mata kallon ita ce tunga ta karshe ga mayakan.

Kamar yadda masu lura da al’amura suka nuna, an samu sassaucin kai hare-haren kungiyar a lokacin da aka tarwatsa su duk da cewa jami’an tsaron Najeriyar sun yi gargadin cewa za a rika ganin daidaikun hare-hare.

Sai dai wannan wa’adi da rundunar sojin Najeriyar ta bayar, yanzu haka ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umar kasar musamman ma a birnin Maiduguri na jihar Borno, jihar da ta fi illatuwa da ta da kayar Boko Haram kamar yadda wakilinmu Haruna Dauda Biu ya tattaro mana.

“Wannan al’amari dai mu dai mun bar wa Allah, amma dai abu guda daya da muka sani shi ne, wato an sha fadar cewa an kama Shekau, ko an kashe Shekau, kuma daga bakin su sojojin mu ke ji, to yanzu kuma an ce an ba da wa’adin kwana 40.” In Ji Malam Hassan Salisu.

“Kamar mu mutanen Borno, mun sha wahala, kuma har yanzu muna kan shan wahala, an ce kamo Shekau nan da kwana 40, Alhamdulillahi, Allah ya tabbatar da wannan abu, Allah ya sa shi ne zai sa mu samu zaman lafiya.” A cewar Malam Aliyu Abdullahi.

Shi kuwa Malam Abubaar cewa ya yi “Allah ya sa wannan Shekau din da za a kama ya zama Shekau na karshe, domin kullum sai ka ji an ce an kashe Shekau… Allah ya sa a kama shi, ko kuma shi da kansa ya kawo kanshi.”

YADDA MASANA HARKAR TSARO KE KALLON WA’ADIN

Su ma masana harkar tsaro a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan wa’adi da Janar Buratai ya bayar, kuma wakilinmu Hassan Maina Kaina da ke Abuja ya jiyo mana ta bakin wasu daga cikinsu.

“Idan har aka samu aka kamo Shekau, ko da yake mun san Shekau din nan, ba yau ake cewa an kama shi ba, amma duk da haka idan aka samu aka kamo shi wannan Shekau din, dole ne wadannan ‘yan ta’addan su sake lale.” A cewar tsohon babban kwamanda a rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Yakubu Usman mai ritaya.

Wasu dai na nuna shakku kan yiwuwar kama Shekau lura da yadda aka kwashe shekaru yana zilliye ma hukumomin Najeriya, amma Farsfesa Al Mustapha Osoji, ya ce abu ne mai yiwuwa.

“Mai yiwuwa ne, saboda shi (Buratai) soja ne kuma ya san menene ya taka, kila bayanan sirri ya zo masu kan yadda za su yi su kama shi, domin duk wanda ka ji ya ce a yi wasan jifa kila ya taka dutse ne. Ta kuma iya yiwu ya gano wani sakaci da rundunar tasa ko kuma wadanda suke tafiyar da ita ke yi.” in Farfesa Osoji.

Sai dai tsohon Hafsan saman sojin Najeriya mai murabus, Aliko El Rashid Haruna, wanda tsohon jami’i ne a hukumar leken asiri ta sojin Najeriya, ya ce ya kamata a yi taka-tsantsan.

“Ba komai ya kamata a fito fili a fadawa ma jama’a ba, in akwai inda yake kuma sun sani bai kamata jama’a su sani ba, sai sun kamo shi sai su fadawa mutane.”

Tun daga shekarar 2009, rikicin Boko Haram ya samo asali inda ya fadada ya kusan mamaye dukkanin jihohin da ke arewa maso gabashin Najeriya da ma wasu yankunan, ya kuma fantsama zuwa wasu kasashe makwabta kamar Kamaru da Nijar da Chadi, lamarin da ya yi sanadin kashe dubun dubatar mutane, kana wasu sama da miliyan guda suka rasa mulallansu.

A lokacin da ya ci zabe a shekarar 2015, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda yanzu haka yake jinya a birnin London, ya sha alwashin kawo karshen rikicin na Boko Haram.

Duk da cewa cikin kusan shekara guda an gurgunta aika-aikacen kungiyar kamar yadda masu lura da al’amura ke fadi, a ‘yan watannin bayan nan ana ci gaba da fama da hare-haren ‘yan kungiyar.

Yanzu dai al’umar Najeriyar za su zuba ido su ga iya gudun ruwan sojojin Najeriya dangane da wannan wa’adi da aka baiwa kwamandojin dake bakin filin daga ko za su iya kawo Shekau da rai ko a mace.

Saurari rahoton wakilanmu Haruda Dauda Biu (Mauduguri) da Hassan Maina Kaina (Abuja) domin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG