Babban daraktan hukumar samarda agajin gaggawa na kasa watau NEMA, Alhaji Yunusa Mai Hajja, ya karyata zargin da wasu ‘yan kudun hijira ke yin a cewea sun kwashe tsawon watanni batare da an samar masu abinci ba da kuma zargin cewa wasu ma’aikatan na karkatar da abinci.
Shugaban hukumar samarda agajin gaggawan yace a ranar 8, ga watan Yuli ne mukaddashi shugaban kasar Najeriya ne Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da rabon kayayyakin abinci ga wadannan al’uma wanda yace kuma wannan bai kai tsawon watanni biyu ba da wadannan mutane ke ikirari.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta ci gaba da ciyar da wadannan mutane domin akwai kayayyaki abinci wadanda aka tanada domin wadannan mutaneyana mai cewa bai ga dalilin da zai sa ace wadannan mutane na kokan rashin abinci ba abinda yace ba gaskiya bane.
Mai Hajja yana mai cewa gwamnatin kasa ta rungumi wannan aiki na ciyar da ‘yan gudun hijira da abinci daban daban kimani tireloli dubu da talatin.
Wasu ‘yan gudun hijira dake sansanin da ake kira Bakasi sun koka da karancin abinci da kuma cin zarafi da suka zargin jami’an tsaro keyi masu.
Facebook Forum