Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Janaral Buhari Alheri da Matsala Ne ga Jam'iyyar APC


APC logo
APC logo

Yayin da jam'iyyar APC ke shirin zaben fitar da gwani, wato dan takarar da zai tsaya mata a zaben shugaban kasar Najeriya, kawunan 'yan jam'iyyar sun soma rabuwa

Abdulmalik Kwamanda na hannun daman Janaral Buhari a Kano kuma jigo a jam'iyyar APC ya mayar da martani akan furucin Abdulmummuni dangane da tsayawar Janaral Buhari zaben shugaban kasa.

Yace Abdulmummuni ba zai so Janaral Buhari ya zama shugaban kasa ba sabili da wani abokinsa dan majalisar tarayya da yake Bauchi. Yace Janaral Buhari shi ne talakawan Najeriya suke so domin shi ne kadai mafitar Najeriya.

Abdulmummuni na magana ne domin Gwamna Rabiu Kwankwaso shi ya tsayar dashi duk da mutane basa sonsa ya zama dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji. Sabili da haka dole ne ya bi bayan maigidansa, wato Rabiu Kwankwaso. Amma yana kuskure idan ya dauki Janaral Buhari daya yake da maigidansa Gwamna Kwankwaso. Nan gaba zai gane shayi ruwa ne.

To saidai masu fashin bakin siyasa sun fara tsokaci akan sarkakiyar dake tafe da zaben fitar da gwani a jam'iyyar APC.

Bashir Hayatu wani mai sharhi ne akan harkokin siyasar Najeriya. Yace Janaral Buhari shi ne alherin jam'iyyar APC kuma shi ne matsalarta. Shi ne alherin jam'iyyar domin idan babu shi inda jam'iyyar ke zaton samu ba zata samu ba. Shi ne kuma matsala domin wasu mutane da suke da karfin yi da fada a ji ba zasu goyi bayansa ba. Amma yana da dimbin magoya bayansa cikin talakawa. Yawancin mutanen arewa dake yin APC kusan kashi 70 suna yi ne dominsa.

Zaben da za'a yi na fitar da gwani mace ce mai ciki. Akwai mai farin jini, akwai dan siyasa, akwai kuma wanda yake da karfin gwamnati. Atiku Abubakar dan siyasa ne. Yasan yadda zai shawo kan mutane ya ci zabe. Shi kuma Janaral Buhari yana da talakawa bayansa amma a wurin fitar da gwani ba talakawa ba ne zasu yi zaben. Rabiu Kwankwaso shi kuma yana ganin yana da karfin gwamnati, da karfin kudi na gwamnati ya nemi zaben. Saboda haka jam'iyyar tana bakin kabari. Tana iya mutuwa kowane lokaci.

Bashir Hayatu ya shawarci 'yan jam'iyyar su lallaba Janaral Buhari ya hakura da shiga takarar zaben. Amma idan ya shiga aka kayar dashi, talakan Najeriya ba zai yadda an kayar dashi ba ne bisa ga zaben gaskiya zai dauka an zalunceshi ne.

Tuni batun fitowar Rabiu Musa Kwankwaso ya fara raba kawunan 'yan jama'iyyar ta APC musamman 'ya'yan kwankwasiya a Kano. Danladi Maifata dan akidar kwankwasiya ne. Shi yana ganin mai girma gwamna Kwankwaso bai kamata ya fito takara ba yanzu saboda sha'awar Janaral Buhari. Kodayake siyasa ce amma akwai tsari na biyayya a dukannin tsarin rayuwa. Janaral Buhari uba ne a cikin tafiyar. Da gudunmawarsa suka ci zaben 2011. Su 'yan kwankwasiya suka kamata su girmama Janarl Buhari.

Amma Abdullahi Rabiu Garindanga wani na hannun daman gwamna Rabiu Kwankwaso yace Janaral Buhari ya rike duk wasu mukamai kuma yayi shugaban kasa. Duniya tana girmamashi. Ya kuma san nagartar Injiniya Rabiu Kwankwaso saboda haka ya bashi takarar kana shi Janaral Buhari ya fito ya zama jagora, wato uban jam'iyyar.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG