Bisa duka alamu shugaban ya inganta harkokin tsaro kamar yadda ya kudura haka ma ya fuskanci yaki da cin hanci da rashawa gadan gadan amma tattalin arziki yana neman ya gagareshi.
Shugaban ya gani cewa da wuya ya iya aiwatar da kasafin kudin bana, wanda aka yiwa coge da dama, dari bisa dari ba idan ba'a yi wani abu ba cikin gaggawa.
A kan batun tabarbarewar tattalin arzikin ne kwamitin da ya kafa dake karkashin mataimakinsa ya bashi shawarar ya nemi ikon kafa dokar ta baci a kasar daga majalisun kasa.
Ba'a taba ba wani shugaban kasa ikon kafa dokar ta baci ba akan tattalin arziki, amma idan aka ba Shugaba Buhari wannan ikon yana iya cimma burinsa cikin 'yan shekarun da suka rage masa a wannan wa'adi na farkon milkinsa.
Shugaban ba zai tsaya yana yin takaddama da 'yan majalisa ba. Amma idan suka bashi wannan ikon zai iya cika alkawuran da ya yiwa kasar akan tattalin arziki.
Ga karin bayani.