Wannan kuwa na faruwa ne inda wasu daga cikin ‘yan majalisar suka kafa wata kungiya ta neman tabbatar da adalci a tsakanin ‘yan majalisar musamman akan al’amuran da suka shafi harkokin kasafi.
Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Hon Abdulmumini Jibril ne ya fara kwarmata wannan zargi akan shugabanin majalisar.
A hirarsa da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari, tsohon shugaban ya bayyana cewa suna bukatar a gudanar da bincike akan irin mutanen dake amfani da wata dama da suke da ita domin yin wasu ayyuka a yankunansu ba tare da sun tuba bukatun sauran ‘yan kasa ba.
Ya kara da cewa abinda ya kamata a yi shine duk wanda bincike ya nuna yayi laifi a nuna masa laifinsa domin hana wasu fara irin wannan hali.
To amma malam Yakubu Musa, mataimaki na musamman ga shugaban majalisar Yakubu Dogara, kan hulda da kafofin yada labarai cewa yayi karamcin fahimtar ayyukan majalisar dokoki game da kasafin kudi ke haifar da wannan cece-kuce.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.