Wakiliyar Muryar Amurka a Jamhuriyar Nijar Tamar Abari, ta ziyarci sashen da ake kula da masu tabin hankali na babban asibitin Damagaram, mafi yawan marasa lafiyar matasa ne kuma shaye shayen kayen maye ne ya haddasa musu juyewar kwakwalwa, a cewar Lawali Girema jami’in dake kula da masu tabin hankali a asibitin.
A cewar Lawali, tabin hankli na wannan zamani mafi yawancin mutanen da ke fama da shi samari ne masu yin shaye shaye, sai kuma wanda ake samu sanadiyar Aljanu da kuma ciwon dake samun mata bayan haihuwa wanda ke taba kwakwalwarsu.
Babban abin yi anan shine hukumomi su kara kaimi wajen yaki da safarar miyagun kwayoyin dake zama ummul aba’isin wannan matsala ga matasa.
Saurari cikakken rahotan Tamar Abari.