Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Gwamnatin Nijar Ta Cafke Motoci 47 Da Direbobi 63 Masu Safarar 'Yan Ci Rani Zuwa Turai


Matuka manyan motocin dakon kaya suka cika kan manyan hanyoyin faransa domin nuna rashin amincewarsu da shirin garambawul din fansho.
Matuka manyan motocin dakon kaya suka cika kan manyan hanyoyin faransa domin nuna rashin amincewarsu da shirin garambawul din fansho.

A cewar ministan tsaron kaar ta Niger Bazun Mohammed dake bitar ayyukan da hukumomi suka aiwatar a tsawon watanni 3 da suka gabata bayan mayar da ‘yan ci rani sama da dubu zuwa garuruwan da suka fito.

Yanzu haka dai gwamnatin ta cafke mutane 47 da suka hada da direbobin jigilar ‘yan ci rani da masu yi musu jagorancin ratsa hamada.

Kana motoci fiye da 63 ne dake jigilar ‘yan cirani sun shiga hannun jamia’an tsaro bayan da aka hango su cikin shirin ketara tsakanin Niger da Libya ko ta bangaren Algeria, wannan yasa Ministan yace zasu huskanci hukuncin da doka tayi tanadi.

Da yake bayyana raayin sa akan matakin hana ‘ya’yan kasashen CEDEWAO ketarawa ta kasar Niger sabo da dalilai na rashin takardu, Mallam Mammam Sani Dan Bala na kungiyar Miyoska mai ofishi a garin Arlik, cewa yayi.

‘’Niger cikin kungiyar CEDEWAO kuma akwai dokoki na wannan kungiyar wadda suka ce kana cikin kasar da take cikin wannan kungiyar, kana dama ka tashi daga wannan kasar zuwa wannan kasar, mutum yazo yace maka daga Bukina Faso yake zai wuce kuma dan kasar da take cikin wannan kungiyar ce, kaga Kenan babu dokar da tace maka ka tsaida shi, idan dai ba ganshi dauke da makami ko kuma wani abu da zai cuta ma kasa bane, Zuwa kawai zaiyi ya wuce, idan ya gitta Niger can kuma gaba abinda ya same shi kansa ya daukar mawa, shima wannan din yakamata ace Africa ta duba ta gani.’’

Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani 3’48

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

XS
SM
MD
LG