Gubar dalma na iya haddasa dimbin illoli, amma illar tafi tsanani akan yara. Duk lokacin da suka yi ta'ammali da dalma, tana takaita yanayin bunkasar kwakwalwar su, tare da illata musu jiki harma ta iya hallaka su," a cewar jami'ar gudanarwar hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) Samantha Powers.
Duk da cewa an fahimci hatsarin dake tattare da gubar dalma, har yanzu kasashen duniya na fama a kan yadda zasu shawo kan barazanar, a cewarta.
"A tarihance, yawan kudaden da ake kashewa duk shekara wajen yaki da annobar gubar dalma a kasashe masu tasowa basu gaza kaiwa dala miliyan 15. Adadin bashi da yawa idan aka kwatanta da abinda ake kashewa a kan cututtuka masu makamantan illoli a kan kiwon lafiya."
Hakan ta sauya a watan da ya gabata, lokacin da Amurka da fiye da masu ruwa da tsaki 50 suka kaddamar da kawancen kawar da annobar gubar dalma anan gaba. Kawancen gwamnatoci da masu bada agaji da kamfanoni sun zuba fiye da dala miliyan 150 da nufin kawo karshen matsalar gubar dalma a tsakanin yara kanana a kasashe masu tasowa kannan da 2040.
Rawar da amurka ke takawa a wannan kawancen wani bangare ne na dabarun da gwamnatoci ke amfani dasu wajen shawo kan matsalolin dake zama barazana a tsakanin yaran duniya, a cewar mataimakin jami'in gudanarwar USAID, Dr. Bama Athreya.
"Hakan yana da mahimmancin gaske saboda mun san cewa duk cikin yara 3 akwai guda 1 dake da tarin gubar dalma a cikin jininsa, kuma hakan na shafar yanayin bunkasar basirarsa tsawon lokaci.
Wannan wata matsala ce da zamu iya yin wani abu a kai kuma irin maida hankalin da dabarun da ake amfani dasu na bada mahimmanci a kan girman yara ne suka bamu damar yin tunani a kan matsaloli irinsu gubar dalma tare da bullo da dabaru na zahiri da kawancen shawo kan matsalar".
Wannan kawancen nada matukar mahimmanci ga manufar Amurka ta bijiro da dabarun da zasu bada kariya ga girman yara a kowane mataki, a cewar mataimakin jami'in gudanarwar USAID Athreya.
"Dabarar fafutuka ta "Thrive" ta duk duniya ce, kuma ta maida hankali ne a kan bunkasa kariya da kula da yaran dake cikin tsanani ko halin rashin galihu a fadin duniya. Abun mamaki game da dabarar ita ce gaba-dayanta mataki ne da gwamnatin Amurka ke dauka a kan yaran dake cikin bukata a fadin duniya."
"Akwai wata faffadar yarjejeniya a kan cewa wajibi ne mu bada kariya ga yaran da basu da galihu a fadin duniya," a cewar mataimakin jami'in gudanarwar Usaid Athreya. Amurka za ta cigaba da aiki tare da kawayenta wajen bada kariya ga yara tare da kawar da duk abinda zai yi tarnaki ga cigabansu.
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.
Dandalin Mu Tattauna