A yayin wata tattaunawa a gefen taron kolin Majalisar Dinkin Duniya (UNGA), Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ayyana cewar, “ta hanyar hakan, dukkanmu zamu gano bukatar karfafa hadin kai a tsakanin kasashen dake yankunanmu domin tabbatar da cewar mutane na yin kaura ta hanyar da ta dace cikin lumana da tsari da tausayi, tare da taimakawa al’umma su rayu…..a kasashensu na asali.”
“Gaba dayanmu, muna saukakawa bakin hauren da suka riga suka ketaro kasarmu samun mataki na doka. Misali, ilahirin gwamnatocin dake yankin na taimakawa ‘yan Venezuela samun matakin samun mafaka a bisa tsarin doka.”
Kasashen Colombia, Ecuador, Peru na sahun gaba, wajen daukar matakan shigar da bakin hauren cikin al’ummomi da tattalin arzikinsu.”
“Sannan muna kokarin kawar da hatsari daga kan hanyoyin da ake bi wajen yin kaura domin hana mutane jefa kawunansu cikin hatsari domin yin balaguro zuwa kan iyakokinmu, a cewar sakatare blinken.
“Mu a nan Amurka, mu muka jagoranci daya daga cikin gangamin fadada yin kaura ta halastacciyar hanya, ciki har da bi ta hanyar ba da agajin sake hada iyalai da shirin yiwa fursunoni afuwa da kuma kara mizaninmu na sake tsugunar da ‘yan gudun hijira 125, 000, a lokaci guda kuma muna karfafa matakanmu na hana yin kaura ta barauniyar hanya,”
Dabarar nan ta yin balaguro cikin lumana (Safe Mobility Initiative) ta baiwa mutanen kasashen yankin Amurka ta Kudu sahihan bayanai da kuma tsarin neman iznin shiga Amurka da ma wasu kasashen ta halastacciyar hanya, ta hanyar amfani da sadarwar zamani.
Haka kuma, Amurka na kokarin dakile harkar safarar mutane da fasa kwabri ta hanyar takaita bada iznin shiga kasar da sanya takunkumi kan hada-hadar kudi.
“Muna yaki da kungiyoyin batagari, sannan muna daukar makamantan wadannan matakai akan kamfanonin dake yin shatar jiragen sama dana ruwa wajen taimakawa yin kaura ta barauniyar hanya,” inji sakatare blinken.
A karkashin Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris, shirin ci gaban yankin tsakiyar Amurka ya samar da fiye da dala biliyan 5.2 ta hanyar zuba jari a bangarorin da bana gwamnati ba a kasashen Honduras da Guatemala da El-Salvador.
Sakatare Blinken ya sanar da cewa Amurka za ta zuba karin jarin fiye da dala miliyan 685 a kasashen Latin Amurka da na yankin Karebiya.
“Wadannan sabbin kudade sun hada da kusan dala miliyan 369 domin taimakawa ‘yan gudun hijira da bakin haure marasa galihu da kuma kasashen dake karbar bakuncinsu, sai kuma dala miliyan 228 domin bada agajin gaggawa ga ‘yan gudun hijirar Venezuela da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu a kasashen Colombia da Ecuador da Peru.
Haka kuma tallafin namu ya samar da dala miliyan 10 ga shirin bankin duniya na samarwa bankuna rangwame a kasashen Latin Amurka da yankin Karebiya.”
“Ina da yakinin cewa gabadayanmu zamu iya matsawa zuwa ga wani mataki da yin kaura zai zama zabin da mutum zai yi cikin ‘yanci kuma a nemi shi da halastacciyar hanya,” a cewar Sakatare Blinken,” kuma inda dukkanin al’umma zasu rayu cikin tsaro da mutunci tare da dimbin damammaki.”
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka
Dandalin Mu Tattauna