Kafar yada labarai ta kasar ta bada rahoton shirin kariya sararin samaniya na Saudiyya, na harbo wani makami mai linzamin a sararin samaniyarta da ke kudu maso yammacin lardi Najran.
A kwanakin baya 'yan tawayen Shi’a na Yemen, wadanda aka fi sani da Houthi, sun auna makamai masu linzami akan Saudi Arabiya. Wanda har Saudi Arabiya ta zargi Iran da laifin marawa 'yan Houthi baya.
'Yan tawayen sun kwace Sanaa babban Birnin Yemen a shekarar 2014, wanda ya tilastawa shugaban kasar da kasashen duniya suka aminta dashi Abd-Rabbu Mansour Hadi haurewa gudun hijirar wucin gadi a Saudi Arabiya.
Dakarun da Saudiyya ke jagoranta sun mayar da martini a watan Maris na shekarar 2015 ta hanyar kai hare-hare da jiragen saman yaki akan 'yan Houthi a madadin gwamnatin Hadi. Hare-haren da ya kashe dubban fararen hula gami da lalata unguwanni ciki har da asibitoci.
Facebook Forum