Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samun Jari Zai Hana Mu Barace-barace - Nakasassu


Wasu masu fama da matsalar makanta a Maiduguri, jihar Borno. Disamba 3 2017. Haruna Dauda Biu
Wasu masu fama da matsalar makanta a Maiduguri, jihar Borno. Disamba 3 2017. Haruna Dauda Biu

Ranar 3 ga watan Disambar kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin dubi kan irin matsalolin da mutane masu fama da nakasa ke fuskanta a duniya.

Mutanen da ke fama da matsalar nakasa a Najeriya, sun yi kira ga hukumomi da suka rika waiwayar matsalolinsu domin su ma a rika damawa da su a harkokin yau da kullum.

Kungiyar nakasassu a Birnin Maiduguri da ke jihar Borno ne ta yi wannan kira, yayin da ake bikin tunawa da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da halin da nakasassu ke ciki.

Ranar 3 ga watan Disamba, ranar ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yi dubi ga irin matsalolin da masu fama da matsalar Nakasa ke ciki.

“Mu kadai ne wadanda ba mu da ofishi na musamman a cikin jihohi 36 a Najeriya, inda za mu rika gabatar da ayyukanmu, saboda haka wannan babban kalubale ne ga jihar Borno.” Inji Malam Umar Muhammed, shugaban gamayyar kungiyoyin nakasassu a jihar.

A cewar Malam Ali Abdu na kungiyar guragu “Ya kamata mu nakasassu tsoffi a taimake mu da kudaden jari ba sai mun hau titi muna bara ba, akwai nakasassu da dama iyayensu sun mutu sun bar su.”

Masu fama da matsalolin na nakasa, sun yi wadannan jawabai ne yayin wani taro da wata kungiyar gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu ta shirya domin wannan rana.

Shi kuwa Ambassador Ahmed Shehu, na shugaban gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu ya yi wannan korafin rashin sanin adadin nakasassu.

"Yau idan kana so ka san adadin nakasassu a jihar Borno, babu wanda zai iya gaya maka, ta yaya za ka iya taimaka musu idan babu sunayensu."

A yayin na sa jawabin, dan majalisar dokokin jihar Borno, Bukar Tijjani, wanda shi ma ya halarci taron, ya ce “koken da muka ji a nan, a matsayina na dan majalisa, za mu tursasa gwamnati wajen ganin an samar da wata doka domin tallafawa nakasassu.”

Taken dai wannan shekara ta 2017 shi ne “samar da sauyi mai dorewa domin ci gaban kowa da kowa.”

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG