Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su taimaka wajen samar da bayanan sirri ga jami’an tsaro saboda a samu damar magance hare-haren ‘yan bindiga.
Buhari ya bayyana hakan yayin da yake nuna takaicinsa kan kisan Capt. Abdulkareem, da ga Sanata Bala Na’ Allah a jihar Kaduna.
“Ina kira ga ‘yan Najeriya da su taimaki jami’an tsaro da bayanan sirri saboda a samu damar hukunta wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda.”
“Mutuwar Abdulkareem, wani mummunan al’amari ne a kalubalen da muke fuskanta kan matsalar tsaro.” Buhari ya ce cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin.
“Ina mai tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa, kudurin da na sa a gaba na kare rayukansu da dukiyoyinsu na nan daram.” Buhari ya ce.
Shugaban na Najeriya ya kuma kara da cewa, wadanda suke taimakawa miyagu da bayanan sirri su san da cewa suna yin illa ne ga al’umominsu akan abin da bai taka kara ya karya ba.
Shugaban Najeriya wanda ya mika sakon ta’aziiyarsa ga iyalan Sanata Bala Na Allah, ya kuma bayyana takaicinsa kan wadanda irin wannan al’amari yake rutsawa da su.
A ranar Lahadi wasu ‘yan bindiga suka kasha Capt. Abdulkarim Na’Allah a gidansa da ke Malali a karamar hukumar Kaduna ta arewa.
Rahotannin sun ce an yi amfani ne da igiya ne aka shake marigayin.