Inda suka tattauna kan muhimman bukatun da yan gudun hijirar da yakin Boko Haram ya daidaita da kuma bukatar dake akwai na gano 'yan matan Chibok da aka sace shekaru biyu da suka gabata.
A tattaunawar da jakadiyar Amurka Samantha Power tayi da manema labaru bayan da ta gama ganawa da shugaba Buhari, tace babu shakka akwai hujjar cewa matsalolin satar mutane da yin garkuwa da su domin azabtarwa yana gaba gaba a jerin abubuwan da suka tattauna.
Power tace dama can Amurka tayi jagoranci sosai wajen samarwa Najeriya bayanan sirri akan ayyuka da bayanan yan kungiyar Boko Haram, da kuma bayar da tallafi na makamai da kuma kayan aiki, na daukar matakan da suka kamata domin murkushe kungiyar Boko Haram.
Saurari cikakken rahotan.