Wani mai bincike kan hakkin dan Adam a Majalisar Dinkin Duniya, ya gano cewa, tsare-tsaren da gwamnatin shugaba Trump ke amfani da su wajen gudanar da harkokin mulki, na kara tilastawa Amurkawa shiga kangin talauci.
Ofishin hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya a jiya Litinin ya ce, Philip Alston, wanda jami’i ne na musamman mai dauko rahoto kan batutuwan da suka shafi tsananin talauci, ya kwashe watanni yana ziyartar sassan Amurka.
Ya kuma hada wani rahoto kan yadda gwamnatocin da suka gabata, suka bar jama’ar kasar cikin halin kunci.
Yayin da yake shirin gabatar da rahoton ga Majalisar Dinkin Duniya a wata mai zuwa, Alston, ya kalublanci gwamnatin shugaba Trump kan matakin da ta dauka na rage kudaden haraji, matakin da ya ce ya bai wa masu hanu da shuni da manyan kamfanoni garabasa, ya kuma kuntatawa talakawa.
Shi dai Alston, ya ziyarci yankunan marasa galihu a Alabama, California, Georgia, Puerto Rico, West Virginia da kuma nan Washington DC.
Sai dai a jiya Litinin, wani jami’in da ke wakiltar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, ya ce, gwamnatin ta Trump, ta dukufa ne wajen samarwa da daukacin jama’ar kasar hanyoyin samun kudaden shiga.
Facebook Forum