Sakatariyar yada labarai ta fadar White House Serah Huckabee Sanders tace ko kusa Shugaban Amurka Donald Trump baya kawo cikas ko kadan ga hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka akan kasar Rasha na game da katsalandan din da ake tuhumar tayi a zaben shugaban kasa na shekarar 2016 wanda ya kawo shugaban kan karagar mulki.
Maimako ma yana fada ne da wannan.
Sanders tana magana ne da manema labarai a jiya Laraba, bayan da shugaba Trump ya bayyana bukatar kawo karshen wannan binciken na musamman.
Trump dai ya ce ne binciken da Robert Mueller ya kwashe watanni 14 yana yi akan alakar Rasha da yakin neman zaben sa wani al’amari ne mara kyau.
Trump yaci gaba da cewa a shafin sa na Twitter ya kamata babban mai shara’a na kasa, Jeff Session wanda yake shine alhakin kula da dokokin kasa ke hannun sa ya dakatar da wannan bita da kullin haka nan kafin yaci gaba da “zubar da martabar kasar mu”.
Facebook Forum