Masana tsaro sun fara nuna damuwa bisa yadda mayakan Boko Haram ke zafafa kai farmaki a sansanonin dakarun Nigeria a shiyar arewa maso gabashin kasar.
Wannan al’amarin ya na kara zaman zullumi ga mazauna yankin.
Air Commander Ahmed Tijjani Baba Gamawa tsohon kwamandan rundunar sojin Nigeria ya bada shawarar “duk lokacin da sojoji suka zauna shekara biyu ko uku, ya kamata a canja su. Domin wadanda suke filin daga su samu zarafin kasancewa da iyalansu kana wasu sum aye gurbinsu”. AHaka kuma yace rashin ba’a biyansu hakkinsu yadda ya kamatazai sa a samu koma baya.
A makon jiya dai ‘yan Boko Haram sai da suka kwace ikon garin Gudunbali na wani dan lokaci kafin sojojin Nigeria su fatattakesu. Ko a baya bayan nan ma sun sha yin rawar gaban hantsi a wasu gagruruwa da ke cikin arewa maso gabas.
To amma Birgediya Maharaji Tsiga ya ce hakan ba koma bay aba ne, nana cewa yakin sari ka nome su ke yi. Idan da suna da rigunan yaki za su fito a yakesu, da an gama dasu tuntuni. Yace an tarwatsa mayakan Boko Haram. Ba su da wani wuri. Ya jaddada cewa sun ruguzasu sai dai yakin sari ka noke da su keyi.
Malam Kabiru Adamu, masanin tsaro ya yi kira a rage nauyin da aka dora kan karfin soja. Yace yakin da ya samo asali akan ra’ayi na addini dole ne a jawo hankalin mazauna yankin su goyi bayan matakan da gwamnati ke dauka. Na biyu a yi kokari a kawar da talauci da ya yi katutu a yankin. Na uku a basu ilimin addini da na zamantakewa.
Kakakin rundunar sojin saman Nigeria Air Commande Ibikunle Daramola y aba da sanarwar rugurguza sanasanonin Boko Haram da jiragen yakinta a Bukarneram da Tundun Allura da ke zirin tafkin Chadi.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum