Masanin tsaro, Malam Kabiru Adamu ya ce ba abin mamaki ba ne saboda wani bangaren Majalisar Dinkin Duniya MDD, ya nuna cewa yawan makaman dake hannun fararen hula a yammacin Afirka da nahiyar Afirka baki daya, ya fi yadda ake zato.
A nasa bangaren tsohon hafsan sojan hukumar liken asirin Nigeria, Aliko El-Rashid Harun ya ce addadin makaman dake hannun waddanda ba jami’an tsaro ba ne ya zarce miliyan 100 da ake harsashe. Ya ce ba za a iya kiyasta addadin makaman dake hannun mutane ba saboda ana shigo da makaman ta barauniyar hanya ba tare da sanin gwamnati ba.
Malam Kabiru Adamu ya yi karin bayani da cewa lamarin na da tada hankali sosai, inda yake cewa duk wata matsalar tsaro da ake fuskanta tana da alaka da waddanan makaman da ake shigo da su ba bisa ka’ida ba, kuma mutane ke mallakarsu ta hanaya mai sauki. Ya ce ya zama wajibi a dau maganar yawan makamai da muhimmanci kana a maida hakali kan iyakokin Nigeria tare da bin wasu hanyoyin magance lamarin.
Facebook Forum