A yanzu dai jihar Nejar na fama da matsalar rashin tsaro a wasu yankunanta a sakamakon yadda yan bindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa su ka addabi yankunan.
Akan haka a l’ummar jihar Nejar ke cike da fatan ganin sabuwar gwamnati ta hanzarta shawo kan wannan matsala a cewar wasu daga cikin al'ummar jihar bayan rantsar da sabuwar gwamnatin.
A cikin jawabinsa, sabon Gwamnan Jihar Nejar Umar Muhammed Bago ya sha alwashin maida hankali wajen tunkarar matsalar rashin tsaron domin shawo kanta kamar yadda ya yi karin bayani in da cewa "za mu hada hannu da jami'an tsaro a matakin kasa dama sauran sassa domin kare dukiya da rayukan yan jihar. "
A can jihar Kwara ma an rantsar da gwamna Abdulrahman Abdurrazak a wa’adi na biyu tare da mataimakinsa Mr. Kayode Alabi a jihar.
Gwamna Abdurrak ya ce zai yi amfani da wa'adinsa na biyu wajen karasa aikin bunkasa tattalin arzikin jihar ta Kwara.
Saurari rahoton Mustapha Batsari: