Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta tura masu bincike zuwa Numan don su binciko musabbabin rikicin da aka yi kwanan nan a yankin Numan; su gano wadanda su ka haddasa shi su kuma bayar da shawara kan irin hukuncin da ya dace kansu.
Kakakin Hedikwatar Rundunar ‘Yan sandan Najeriya CSP Jimoh Mooshud ya tabbatar da cewa Sufeto-Janar na ‘yansandan Najeriya ya cika alkawarin da ya yi na tabbatar da cewa an gudanar da bincike a matakin tarayya saboda ya tura masu bincike zuwa inda tashin hankalin ya faru. Hukumar ta ‘yan sanda ta sake yin gargadi ga duk wanda ya sake tayar da zaune tsaye
Wani shugaban Fulani makiyaya a Najeriya, Alhaji Dodo Oroji ya goyi bayan wannan mataki. Y ace muddun ana hukunta masu haddasa fitina to lallai za a takaita tashe-tashen hankula a Najeriya. Shugaban matasan arewacin Najeriya Imrana Wada Nas y ace an sha kafa kwamitin bincike bayan tashin hankali to amma idan aka ga cewa wadanda su ka haddasa shafaffu ne da mai sai a kyale su. Wannan, inji shi, shi ke hana shawo kan fitina a Najeriya.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Facebook Forum