Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Dangantakar Amurka Da Masar


Shugaba Sisi (Hagu) Da Shugaba Trump (Dama) a Lokacin Da Ya Kawo Ziyara Washington
Shugaba Sisi (Hagu) Da Shugaba Trump (Dama) a Lokacin Da Ya Kawo Ziyara Washington

A iya cewa tsawon lokacin da aka kwashe ba tare da an ga wani shugaban Masar ya kawo ziyara Amurka ba ya kawo karshe a jiya Litinin bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya karbi bakuncin takwaran aikinsa na Masar Abdel Fattah al Sisi.

Rabon da wani shugaban Masar ya kawo ziyara Washington, tun a zamanin tsohon shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2009.

A lokacin wannan ziyara ta Sisi, kalaman shugaba Trump, kamar yadda wasu masu fashin baki suka lura, a iya cewa sun kawo karshen tsatstsamar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tun bayan da Sisi wanda tsohon Janar ne tare da dakarun kasar suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Mohamed Morsi.

Shi ma Sisi ana shi bangaren, ya yaba wa shugaba Trump kan irin matakan da yake dauka na yaki da ayyukan ta’addanci.

Yayin taron manema labarai, kakakin Fadar White House, Sean Spicer, ya ce shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwan da suke da banbancin ra’ayi da akasin haka.

Tsohon jakada David Mack, wanda yanzu Malami ne a Cibiyar Nazarin harkokin Yankin Gabas Ta Tsakiya, wato Middle East Institute a turance, ya fada wa Victor Beattie na Muryar Amurka cewa bai yi mamaki da yadda shugabannin biyu suka samu fahimtar juna, saboda suna da kusan manufofi iri daya.

Mack ya kuma kara da cewa, wadanda suke tunanin tattaunawar za ta fi maida hankali ne kan kira ga Masar ta kara kaimi kan batutuwan kare hakkin bil adama, sun sha mamaki.

A cewarsa, gwamnatin ta Trump ta fi maida hankali ne kan yadda za a yi yaki da kungiyar IS da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG