A wani taron manema labarai da shugaban kwamitin kula da harkokin ma’aikata na majalisar ya kira Abdul Malik Boso, yace majalisar ba ta gamsu da wannan mataki ba kuma bata yarda da hujjojin gwamnatin jihar Niger ba, na cewa rashin kudi ne yasa aka biya ma’aikatan rabin albashinsu.
Shima shugaban marasa rinjaye na Majalisar Bello Agwara, ya tabbatar da matsayin majalisar kan wannan batu, inda yace hakki ya rataya ga gwamnati wajen tsayawa dubi hanyar da zata sami kudi ta biya ma’aikatanta.
A halin da ake ciki dai kungiyar kwadagon jihar ta ja daga, har ta fara raba takardun cewa zata fara wani yajin aiki mai zafi daga ranar Litinin mai zuwa, har sai gwamnatin jihar ta janye sabon tsari na biyan ma’aikata rabin albashinsu.
Saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.