Kakakin rundunar tsaro a jihar Plateau ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka cewa daukar matakan tsaron a wannan karon ya zama dole musamman ma saboda wasu hatsaniya da aka rika samu tsakanin wasu matasa a birnin Jos, har yayi sanadin rasa rai guda.
Jami’an babban masallacin garin Jos ma sun dauki matakan tsaro domin ganin an gudanar da bukin sallah lafiya. Alhaji Sabo Shu’aibu, shine mai kula da harkar tsaro a kungiyar Jama’atu reshen jihar Plateau, yace babu wata mota da zata kusanci masallaci domin duk motoci zasu tsaya mita 500 da masallacin.
Haka kuma kafin shiga masallaci akwai guraren bincike har hudu domin tabbatar da cewa mutum baya dauke da wani abu jikinsa.
A wani rahoto da Muryar Amurka ta samu na cewa ‘yan ta’adda na shirin kai wasu hare hare a Majami’u da Kasuwanni da guraren shakatawa da sauran guraren da ake samun taruwar jama’a.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji.